Rahoton Planet Football ya nuna cewa duk da yawan jama’a da kuma shauƙin wasan ƙwallon ƙafa, wasu ƙasashe har yanzu ba su taɓa buga gasar Kofin Duniya ta FIFA World Cup ba.
Ƙasar India ce ke kan gaba a jerin ƙasashen da ke da yawan jama’a amma ba su taɓa shiga gasar ba. Duk da cewa Indiya ta samu tikitin shiga gasar ta 1950, ta janye kafin a fara gasar, kuma har yanzu ba ta taɓa buga wasan ba.
Jerin ƙasashen
1. India — mutane biliyan 1.4
2. Indonesia — miliyan 278
3. Pakistan — miliyan 243
4. Bangladesh — miliyan 169
5. Ethiopia — miliyan 125
6. Philippines — miliyan 113
7. Vietnam — miliyan 99
8. Thailand — miliyan 71
Dalilin rashin shiga gasar
Masana sun ce akwai dalilai da dama da suka haɗa da ƙarancin zuba jari a harkokin kwallon ƙafa da rashin ingantaccen tsarin horaswa da ƙarancin filayen wasanni, da kuma fifikon wasu wasanni a wasu ƙasashen.
Misali, a ƙasashe kamar Indiya da Pakistan da Bangladesh, wasan cricket ya fi shahara fiye da ƙwallon ƙafa.
A ɓangaren Afirka kuwa, ƙasar Ethiopia ta fi kusan kaiwa mataki mai nisa a neman shiga gasar ta 2014, inda ta kai zagayen ƙarshe na neman tikiti amma ta sha kashi a hannun Nigeria.
Wannan rahoto yana nuna cewa yawan jama’a kaɗai ba ya tabbatar da nasara a ƙwallon ƙafa, sai an haɗa shi da ingantaccen horo da zuba jari da kuma tsarin ci gaban matasa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment