Trump Ya Ce Iran Ta Harbo Jirgin Sojin Amurka A Tekun mashigar ruwan Hormuz.

Trump Ya Ce Iran Ta Harbo Jirgin Sojin Amurka A Tekun mashigar ruwan Hormuz.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Iran ta harbo wani jirgin helikwafta na sojin Amurka (Apache) yayin da yake sintiri a yankin Tekun mashigar ruwan Hormuz cikin dare.

Rahoton da aka danganta ga kamfanin labarai na Reuters ya ce Trump ya yi wannan bayani ne kan abin da ya faru a yankin a lokacin da ake samun tashin hankali a Tekun Fasha.

Trump ya ce Amurka “ba makawa dole ta mayar da martani” kan wannan abin da ya kira hari.

Sai dai har yanzu babu cikakken tabbaci daga hukumomin Amurka ko Iran kan ko an harbo jirgin da gaske, ko kuma ya fadi ne saboda wani dalili daban. 
Rahotanni na baya-bayan nan sun ce an ceto matukan jirgin biyu kuma suna cikin koshin lafiya.

Lamarin ya kara tayar da hankali a yankin, kasancewar Tekun Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

0 $type={blogger}: