Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da cewa an kashe jami’an tsaro uku a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Kasa (NIPSS), da ke Kuru.
An kai harin ne da sanyin safiyar Litinin, inda aka kai wa jami’an tsaron da ke bakin aiki a cibiyar hari.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, SP Alfred Alabo, ya fitar ranar Talata, rundunar ta bayyana bakin cikinta kan lamarin.
Sanarwar ta ce: “Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da faruwar lamarin da ya shafi jami’an tsaro da ke bakin aiki a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Kasa, NIPSS dake Kuru. Abin takaici, jami’an tsaro uku sun rasa rayukansu yayin harin.”
Rundunar ta ce an kara tura jami’an tsaro zuwa yankin tare da kara yawan sintiri a kusa da cibiyar da sauran wuraren da ke makwabtaka da ita.
‘Yan sandan sun tabbatar wa mazauna yankin cewa an dawo da zaman lafiya, kuma harkokin yau da kullum sun ci gaba.
Sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka kai harin, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin doka.
NIPSS Kuru ita ce babbar cibiyar Najeriya da ke horas da manyan jami’an gwamnati kan manufofi da dabarun tafiyar da kasa. Harin ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin tsaro da aka taba fuskanta a cibiyar a ‘yan shekarun nan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment