Sakamakon karuwar matsalar tsaro a wasu sassan Jihar Katsina, Gwamnatin Jihar ta sanar da daukar wasu tsauraran matakai domin dakile matsalolin tsaro.
Daga cikin matakan da aka dauka akwai haramta safarar ko amfani da man fetur a cikin jarkoki, tare da bayar da umarnin rufe dukkan wuraren hada-hadar kudi na POS da kuma na cajin waya a kananan hukumomin Matazu da Musawa nan take.
Haka kuma, gwamnatin ta haramta amfani da babura a wadannan yankuna a matsayin wani bangare na kokarin inganta tsaro da rage barazanar aikata laifuka.
An bukaci mazauna yankunan da su bi umarnin gwamnati tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment