Tunisiya Ta Kori Kocinta, Lamouchi Bayan Wasan Daya Kacal a Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA 2026.

Tunisiya Ta Kori Kocinta, Lamouchi Bayan Wasan Daya Kacal a Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA 2026.

Ƙasar Tunisiya ta kori kocinta Sabri Lamouchi bayan wasa ɗaya kacal a gasar cin kofin duniya ta 2026, bayan da ta sha kashi da ci 5–1 a hannun Sweden.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Tunisiya ta sanar cewa kocin Faransa,Hervé Renard ne zai maye gurbin Lamouchi, kuma zai jagoranci tawagar har zuwa ƙarshen gasar.

Renard, wanda ya jagoranci Saudi Arabia ta samu gagarumar nasara a kan Argentina a gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka gudanar a Qatar, ya dawo fagen horar da ƙwallon ƙafa ta maza bayan ya taɓa jagorantar tawagar mata ta Faransa.

Lamouchi mai shekaru 54, an naɗa shi a matsayin koci ne a watan Janairu, kuma ya samu nasara a wasa ɗaya cikin wasanni biyar da ya jagoranta — nasarar ci 1–0 a kan Haiti.

Babban rashin nasarar da Sweden ta jefa wa Tunisiya ya sa aikin samun gurbin zuwa zagayen gaba ya zama mai wahala. Za su kara da Japan a wasan rukuni na F, kafin su fuskanci Netherlands.

0 $type={blogger}: