Rundunar ’yan sandan jihar Abia ta cafke wani mutum da aka gani yana cin zarafin wata mata a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.
Jami’an sashen yaki da manyan laifuka (VCRU) na rundunar ’yan sandan jihar Abia ne suka gudanar da kama mutumin bayan samun sahihan bayanai kan inda yake.
An ce jami’an ’yan sanda karkashin jagorancin Babban Sufeto na ’Yan Sanda (CSP) Emeka Amanchukwu ne suka jagoranci aikin kama shi.
An kama wanda ake zargin ne a yankin Ogbor Hill da ke Aba a ranar 20 ga watan Yuni.
Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan sandan sun dauki mataki cikin gaggawa bayan samun bayanan sirri, lamarin da ya kai ga gano shi da kuma kama shi.
Wata majiya ta ce: “A yanzu haka wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.”
Sashen VCRU ya sake jaddada cewa zai ci gaba da kokarin gano masu aikata laifukan ta’addanci da tashin hankali da kama su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment