NDLEA Ta Kama Tsofaffi Biyu Da Ake Zargi Da Sayar Da Kwayoyi Ga Daliban makarantar Sakandare.

NDLEA Ta Kama Tsofaffi Biyu Da Ake Zargi Da Sayar Da Kwayoyi Ga Daliban makarantar Sakandare.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wasu tsofaffi biyu a jihar Abia bisa zargin sayar da miyagun kwayoyi ga daliban sakandare.

Wadanda aka kama sun hada da Godfrey Orji mai shekaru 84 da Godwin Obulunbiya Obiora mai shekaru 75, wadanda aka kama a Umuahia yayin wani samame da hukumar ke gudanarwa a fadin kasar.

A cewar NDLEA, an kama Obiora ne a ranar 19 ga Yuni, 2026, bayan samun bayanan sirri cewa yana sayar da miyagun kwayoyi, ciki har da magungunan da ke dauke da sinadarin opioid, daga wani shagon sayar da magunguna a Club Road, Umuahia.

Hukumar ta ce binciken shagon ya kai ga gano wasu kwayoyi masu nauyin kilogiram 4.64, ciki har da tramadol da diazepam.

A wani bangare kuma, an kama Orji, wanda tsohon ma’aikaci ne da ya yi ritaya, bayan jami’an tsaro a makarantar sakandire ta Saint Silas, Old Umuahia, sun zarge shi da bai wa wasu dalibai matasa kwayoyi.

Daya daga cikin daliban, mai shekaru 15 da ke aji SS2, ya bayyana cewa tsohon mutumin ne yake ba shi kwayoyin, wadanda shi kuma yake rarrabawa ga wasu dalibai.

NDLEA ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, yayin da daliban da lamarin ya shafa za a sanya su cikin shirin ba da shawarwari da gyaran hali.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta gudanar da wasu manyan samame a sassan kasar, inda ta kama wasu masu safarar kwayoyi tare da kwace miyagun kwayoyi masu yawa.

Shugaban NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yabawa jami’an da suka gudanar da ayyukan, tare da bukatar su ci gaba da yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safararsu a Najeriya.

0 $type={blogger}: