Iran Ta Ce Ba Za Ta Sake Bude Mashigar ruwan Hormuz Ba Har Sai An Tsagaita Wuta a Lebanon.

Iran Ta Ce Ba Za Ta Sake Bude Mashigar ruwan Hormuz Ba Har Sai An Tsagaita Wuta a Lebanon.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim dake Iran ya ruwaito cewa, Iran ba za ta sake bude Mashigar ruwan Hormuz ba har sai an tabbatar da cikakken mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Lebanon.

Rahoton, wanda ya ambato wani tushe da ke kusa da tawagar masu tattaunawar Iran, ya ce mashigar ruwan za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an fitar da izinin da zai bai wa Iran damar sayar da danyen mai.

Mashigar ruwan Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma duk wani cikas a cikinta na iya shafar kasuwannin makamashi na duniya.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kokarin diflomasiyya na shawo kan rikicin da ya shafi Iran da Isra’ila da Lebanon.

0 $type={blogger}: