‘Yan majalisar wakilai na jam’iyyun adawa sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da matsin tattalin arziki a ƙasar, ko kuma ya sauka daga mulki.
Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Majalisar Tarayya da ke Abuja, inda suka zargi gwamnatin Tinubu da fifita shirye-shiryen siyasa na shekarar 2027 fiye da matsalolin da ke damun ‘yan ƙasa.
Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Fred Agbedi, ya ce Najeriya na fuskantar matsalar rashin tsaro mai tsanani da matsin tattalin arziki da kuma barazana ga dimokuraɗiyya.
Ya buƙaci Shugaban Ƙasa ya dakatar da harkokin siyasar 2027 tare da ƙaddamar da wani shiri na watanni shida domin farfaɗo da tsaro da tattalin arziki.
‘Yan majalisar sun nuna damuwa kan yawaitar hare-hare da sace-sacen mutane a jihohi da dama ciki har da Borno da Oyo, Kogi da Filato da Kwara da Neja da Binuwe da Sakkwato da Zamfara.
Sun kuma yi Allah-wadai da sace tsohon Janar na Sojojin Najeriya, Manjo-Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), wanda daga baya aka samu labarin rasuwarsa.
Agbedi ya ce: “Idan Janar ba shi da tsaro a cikin ƙasar nan, to wa ke da tsaro?”
Sun ce ci gaba da tsare ɗalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo alama ce ta gazawar gwamnati wajen kare jama’a.

0 $type={blogger}:
Post a Comment