Farashin Mai Ya Sauka da Kashi 2% Bayan Rattaba hannu kan Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta Tsakanin Amurka da Iran

Farashin Mai Ya Sauka da Kashi 2% Bayan Rattaba hannu kan Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta Tsakanin Amurka da Iran

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya ragu da sama da dala guda kan kowace ganga a ranar Alhamis, bayan Amurka da Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniyar wucin gadi ta tsagaita bude wuta da ake sa ran za ta kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu, tare da bude mashigar ruwan Hormuz domin jigilar mai.

Farashin man Brent ya sauka da kashi 2.06% zuwa dala 77.91 kan kowace ganga, yayin da man Amurka WTI ya ragu da kashi 2.34% zuwa dala 74.99 kan kowace ganga.

Yarjejeniyar mai dabtari 14 ta fara wani zangon tattaunawa na kwanaki 60, inda aka shirya dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz, wadda ke daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai da iskar gas a duniya.

Masana harkokin kasuwanci sun ce masu zuba jari na sa ran dawowar karin man Iran zuwa kasuwannin duniya idan yarjejeniyar ta dore, lamarin da zai iya kara saukar da farashin mai.

Sai dai wasu manazarta sun yi gargadin cewa dawowar man ba za ta kasance cikin gaggawa ba, saboda wasu kamfanonin jigilar kaya har yanzu suna nuna fargaba kan dorewar yarjejeniyar.

Yarjejeniyar ba ta warware dukkan manyan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu ba, ciki har da batun shirin nukiliyar Iran, inda ake sa ran ci gaba da tattaunawar.

Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) ta gargadi cewa idan yarjejeniyar ta yi nasara kuma aka dawo da fitar da man Iran yadda ya kamata, kasuwar mai na iya fuskantar yawan wadata a shekarar 2027.

Har ila yau, hasashen cewa Babban Bankin Amurka (Fed) na iya kara yawan kudin ruwa a bana ya kara matsin lamba kan farashin mai, saboda hakan na iya rage ci gaban tattalin arziki da bukatar makamashi.

0 $type={blogger}: