Wani harin jirage marasa matuka da Ukraine ta kai a wurare da dama a birnin Moscow na ƙasar Rasha, ya haddasa gobara a wani babban matatar mai tare da haifar da hayaki mai yawa a sararin birnin.
Rahotanni sun ce harin ya shafi matatar mai da ke yankin Kapotnya, lamarin da ya kawo tsaiko ga ayyukan matatar tare da tilasta wasu filayen sauka da tashin jiragen sama a Moscow dakatar da zirga-zirga na wani lokaci.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce harin wata “amsa mai adalci” ce ga hare-haren da Rasha ke kaiwa garuruwan Ukraine.
Magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin, ya ce rundunar tsaron sararin samaniyar Rasha na mayar da martani ga wani babban harin Jirgin sama mara matuki, inda ya yi ikirarin cewa an kakkabo daruruwan jirage marasa matuka.
Harin ya zo ne bayan da Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan birnin Kyiv da wasu sassan Ukraine. Bangarorin biyu na ci gaba da zargin juna da kara tsananta rikicin, yayin da suke musanta kai hare-hare da gangan kan fararen hula.

0 $type={blogger}:
Post a Comment