Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2.3 Na Kudin Shiga da aka samu a watan Mayu 2026.

Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2.3 Na Kudin Shiga da aka samu a watan Mayu 2026.

Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi sun raba jimillar Naira tiriliyan 2.3 a matsayin kudaden shiga na watan Mayun shekara 2026.

Kwamitin Rarraba Kudin Asusun Tarayya (FAAC) ne ya bayyana hakan bayan taron watan Yuni 2026 da aka gudanar a Abuja.

Daraktan Yada Labarai na Ofishin Babban Akanta-Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ya ce kudaden da aka raba sun kunshi Naira tiriliyan 1.611 daga kudaden haraji na doka da kuma Naira biliyan 688.785 daga harajin VAT.

FAAC ta bayyana cewa jimillar kudin shigar da aka samu a watan Mayu 2026 ya kai Naira tiriliyan 3.395, yayin da aka cire kudaden gudanarwa da wasu kudaden canja wuri da diyya.

Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 818.680, jihohi sun samu Naira biliyan 759.141, yayin da kananan hukumomi suka samu Naira biliyan 534.277.

Haka kuma, an raba Naira biliyan 188.132 na kashi 13 cikin 100 na kudaden albarkatun kasa ga jihohin da suka cancanta.

Kwamitin ya kara da cewa kudaden harajin doka sun karu zuwa Naira tiriliyan 2.651 a watan Mayu, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 2.378 a watan Afrilu.

Sai dai kudaden VAT sun ragu daga Naira biliyan 806.617 a Afrilu zuwa Naira biliyan 743.668 a waran Mayu 2026.

0 $type={blogger}: