Mazauna birnin Yamai, babban birnin Nijar, sun ce an ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman birnin da safiyar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa an fara jin karar bindigogi da misalin ƙarfe 6:00 na safe a bakin ƙofar filin jirgin, kuma harbin ya ci gaba na kusan sa’o’i biyu. Wasu mazauna yankin sun ce karar harbin na fitowa ne daga wajen ƙofar filin jirgin.
Wannan lamari ya faru ne watanni bayan wani babban hari da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya suka kai kan filin jirgin a watan Janairu.
Ƙungiyar Daular Musulunci a yankin Sahel ta ɗauki alhakin harin, amma sojojin Nijar tare da taimakon wasu mayaƙan Rasha suka dakile shi.
Bayan harin na Janairu, hukumomi sun rushe dubban gidaje da aka gina ba bisa ka’ida ba a wata babbar unguwa kusa da filin jirgin, suna zargin cewa mayakan ƙungiyoyin ta’addanci sun kutsa cikin yankin domin shirya harin.
Nijar, wadda take yankin Sahel na Afirka ta Yamma, ta shafe shekaru tana fama da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da suka haɗa da masu alaƙa da Kungiyar Al-Qaeda da masu Ikirarin kafa Daular Musulunci.
Har zuwa yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan harbin na baya-bayan nan ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment