Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin soke Hukumar Kula da Jarabawar Larabci da Nazarin Addinin Musulunci ta Ƙasa (NBAIS).
Ma’aikatar Ilimi ta ce labaran da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta kan batun ba gaskiya ba ne, kuma ba su da tushe.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar, gwamnati ta ce ba ta gabatar da wani ƙuduri a Majalisar Ƙasa da nufin soke NBAIS ba, haka kuma ba ta ƙaddamar da wata manufa da za ta dakatar da ayyukan hukumar ba.
Ma’aikatar ta bayyana cewa NBAIS har yanzu tana nan a matsayin hukumar jarabawa da ba da takardar shaidar kammala karatu, wadda ke kula da tsare-tsare da inganta ilimin Larabci da na addinin Musulunci a Najeriya.
Gwamnatin ta kuma tabbatar wa jama’a cewa tana ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin ilimi da na jarabawa da aka kafa bisa doka, tare da bin manufofin ilimi na ƙasa.
Game da NBAIS:
Hukumar NBAIS wata hukuma ce ta gwamnatin tarayya da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi. An kafa ta a shekarar 1960 domin kula da makarantun Larabci da na addinin Musulunci a Arewacin Najeriya, daga baya kuma ta samu cikakkiyar amincewa a matsayin hukumar jarabawa.
Hukumar tana gudanar da jarabawa daban-daban ciki har da jarabawar kammala Sakandaren Larabci da Nazarin Addinin Musulunci (SAISSCE) da kuma jarabawar Tahfeez ga ɗaliban da suka ƙware wajen haddar Alƙur’ani da ilimansa. Takardun shaidar hukumar ana karɓarsu a manyan makarantun Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment