Shugaban Taiwan, William Lai Ching-te, ya ce yana fatan Amurka za ta amince da shirin sayar da makamai ga Taiwan mai darajar dala biliyan 14 cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa tsibirin ba zai amince da haɗewa da China ba.
Taiwan ta dogara sosai da tallafin Amurka domin ƙarfafa tsaron ta daga yiwuwar wani hari daga China, yayin da Washington ke matsa wa Taipei lamba ta ƙara yawan kuɗin da take warewa bangaren tsaro.
Sai dai sayar da makaman na ƙara samun tsaiko a dangantakar Amurka da China. Beijing na kallon Taiwan a matsayin wani yanki nata, kuma ta ƙara matsin lamba na soja da diflomasiyya kan tsibirin.
A watan Mayu, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce ana ci gaba da duba yarjejeniyar sayar da makaman.
Da yake jawabi a taron manema labarai na ƴan jaridun ƙasashen waje a Taipei, Shugaba Lai ya ce yana son tattaunawa da China bisa “daidaito da girmamawa”, amma ya ce makomar Taiwan a hannun mutanen Taiwan take.
Ya ce kare tsaron ƙasar Taiwan da kiyaye tsarin dimokuraɗiyya da ƴancin rayuwa ba wani tsokana ba ne ga China.
Taiwan ta ce alkawarin Amurka na tallafa mata bai sauya ba, saboda dokar Amurka ta bukaci samar da hanyoyin da Taiwan za ta kare kanta.
Ma’aikatar Tsaron Taiwan ta kuma bayyana cewa tana shirin gabatar da wani sabon shirin tsaro na musamman mai darajar dala biliyan 6.64 domin sayen na’urorin sa ido da ƙananan jirage marasa matuƙa.
Shugaba Lai ya yi kira ga China da ta daina barazanar amfani da ƙarfi a yankin tekun Pasifik, yana mai cewa sayen makaman Taiwan na aika saƙo ga duniya cewa tana shirye ta kare kanta.

0 $type={blogger}:
Post a Comment