An shiga rudani a jihar Kwara bayan wasu ‘yan bindiga sun sace wani jigo a kungiyar Oodua Peoples Congress (OPC), Comrade Bayo Fabiyi, tare da wasu mutane biyu a garin Oko-Irese da ke karamar hukumar Irepodun.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace Fabiyi tare da direba da wani abokin tafiyansu yayin da suke kan hanyarsu domin kai kudin fansa da wasu kayayyaki don neman sakin wani mutum da aka sace a baya.
Majiyoyi sun ce tawagar tana dauke da kusan naira miliyan 30 da babura guda biyar da buhunan shinkafa guda uku lokacin da ‘yan bindigar suka tare su.
An ce tafiyar tana da alaka da kokarin ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a wannan yankin.
Wata majiya ta ce an kashe mutumin da aka sace tun farko kafin tawagar kai kudin fansar ta isa wurin, amma ba su san hakan ba.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun ja wadanda suka sace zuwa wani daji da ke kan hanyar Kwara zuwa Kogi.
Haka kuma an ruwaito cewa Fabiyi ya samu shawarar kada ya yi wannan tafiya, amma ya ki daukar shawaran.
Da aka tuntubi Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya ce rundunarsa ba ta samu wani rahoto na hukuma game da sace wani jami’in OPC ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa ‘yan sanda za su fara bincike da zarar an gabatar da korafi a hukumance.

0 $type={blogger}:
Post a Comment