Wata babbar kotu a Zimbabwe ta wanke fitacciyar ‘yar jarida Faith Zaba bayan shafe kusan shekara guda tana fuskantar shari’a kan wani rubutu na barkwanci da ya soki Shugaban ƙasar Emmerson Mnangagwa.
Zaba, wacce ita ce editan jaridar Zimbabwe Independent, an kama ta ne a watan Yulin shekaran 2025 bayan ta wallafa wani rubutu mai taken “Lokacin Da Ka Zama Ƙasar Mafia” a sashen barkwanci na jaridar.
Masu gabatar da ƙara sun zarge ta da ƙoƙarin raunana ikon shugaban ƙasa, suna cewa rubutun nata na iya haddasa ƙiyayya ga shugaban mai shekaru 83.
Sai dai Babbar Kotun Harare ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi mata, kamar yadda ƙungiyar lauyoyin kare hakkin ɗan Adam ta Zimbabwe (ZLHR) ta bayyana.
Ƙungiyar ta ce hukuncin wata nasara ce ga ‘yancin aikin jarida da kuma haƙƙin jama’a, tare da zargin cewa hukumomi sun wuce gona da iri wajen amfani da doka.
Zaba ta ce wannan hukunci ya kawo ƙarshen doguwar shari’ar da ta haɗa da tsare ta a gidan yarin Chikurubi da kuma yawan zuwa kotu.
Ta gode wa mutanen da suka tsaya mata a lokacin da take fuskantar wannan matsala.
A gefe guda, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da jam’iyyun adawa sun zargi gwamnatin Shugaba Mnangagwa da amfani da dokoki wajen dakile masu suka da zargin da gwamnati ta musanta.
Wani ɗan jarida mai suna Blessed Mhlanga shi ma ya fuskanci kamu, bayan an zarge shi da tayar da hankali saboda wata hira da ya yi da wani mai sukar gwamnati.
Mnangagwa ya zama shugaban ƙasa ne a shekarar 2017 bayan sojoji sun hambarar da tsohon shugaban ƙasar Zimbabwe, Robert Mugabe, Inda ya lashe zaɓe a shekaran 2018 da kuma 2023.
Masu suka na zargin wasu na ƙoƙarin tsawaita mulkinsa bayan shekarar 2028, yayin da batun gyaran kundin tsarin mulki ya jawo cece-kuce a ƙasar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment