Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Biyu, tare da Kama Wasu Hudu a jihar Kaduna.

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Biyu, tare da Kama Wasu Hudu a jihar Kaduna.

Rundunar haɗin gwiwa ta tsaro ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma (OPFY), ta ce dakarunta sun hallaka wasu ‘yan bindiga biyu, sannan sun kama wasu huɗu, tare da kwato dabbobin da aka sace a wasu hare-haren haɗin gwiwa da suka gudana a Jihar Kaduna.

Ayyukan tsaron da aka gudanar tsakanin ranar 20 zuwa 21 ga watan Yuni sun mayar da hankali ne kan fatattakar ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka haɗa da ‘yan fashin daji da masu ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.

Rundunar sojin ta bayyana cewa ta samu sahihan bayanan sirri kan wasu masu satar shanu a wani kauye da ke Kaduna, inda dakarunta suka yi gaggawar kai farmaki tare da tsare masu laifin.

Hakan ya haifar da musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindigan, inda aka kashe mutum biyu daga cikinsu. An kuma samu nasarar kwato dabbobin da aka sace, makamai da alburusai.

Sai dai rundunar ta ce wani farar hula ya rasa ransa a yayin lamarin sakamakon abin da ta danganta da ayyukan ‘yan bindigan.

A wani samame na daban da aka gudanar da daddare, sojoji sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ‘yan bindiga da masu ta’addanci. 
An samu wasu na’urorin sadarwa daga hannunsu waɗanda ake zargin suna ɗauke da bayanan da za su taimaka wajen bincike.

A ranar 21 ga watan Yuni kuma, dakarun sun yi arangama da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai, inda suka tsere zuwa daji saboda matsin lambar sojoji. 
Daga bisani an kama wasu mutane biyu da ake zargin masu leƙen asiri ne ga ƙungiyoyin masu laifi.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da babura da na’urorin sadarwa masu ɗauke da bayanan da ake bincike a kai.

Haka kuma, an tura sojoji zuwa yankin Mararraba a Kaduna bayan tashin hankali ya barke sakamakon kashe wata mata da ake zargi da safarar yara da wasu fusatattun mutane suka yi.

Sojojin sun tarwatsa jama’ar, sun kare muhimman wurare tare da tabbatar da an dawo da zaman lafiya da zirga-zirga a yankin.

Kwamandan Operation Fansan Yamma ya yabawa dakarun bisa jajircewarsu, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-haren sirri da na musamman domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da inganta tsaro a Arewa maso Yamma.

0 $type={blogger}: