Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali na Kuje.
An umurci a ci gaba da tsare Sowore har zuwa ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
Matakin ya biyo bayan ƙarar tuhume-tuhume biyu da Hukumar SSS (DSS) ta shigar a kansa, inda take zarginsa da aikata laifin amfani da kafafen sadarwa wajen tsangwama da kuma ɓata suna, bayan ya kira Shugaba Bola Tinubu da kalmar “mai laifi” a wani saƙon da ya wallafa a kafar sada zumunta a watan Agustan 2025.
Sowore ya ƙi goge saƙonnin nasa, yana mai cewa yana da haƙƙin faɗar albarkacin baki.
A watan Mayun 2026, Mai shari’a Mohammed Umar ya yi watsi da buƙatar Sowore ta dakatar da shari’ar, inda ya ce DSS ta gabatar da isasshen hujja da ke buƙatar ya kare kansa a kotu.
A farkon watan Yuni, lauyoyin Sowore sun janye daga shari’ar bayan sun ce an wulakanta su yayin zaman kotu. Daga baya Sowore ya yanke shawarar kare kansa, tare da zargin alkalin kotun da nuna son kai.
A ranar 16 ga Yuni, 2026, masu gabatar da ƙara sun zargi Sowore da ƙoƙarin jinkirta shari’ar bayan bai bayyana a zaman da aka tsara domin ci gaba da gabatar da kariya ba. Daga nan kotun ta soke belinsa tare da bayar da umarnin kama shi.
Yanzu haka kotun ta umurci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da shari’ar ke ci gaba.
Gwamnatin Tarayya ta dogara ne da tanadin Sashe na 24 na dokar laifukan yanar gizo da aka yi wa gyara a shekarar 2024, inda masu gabatar da ƙara ke cewa kalaman Sowore a intanet ƙarya ne kuma suna iya haddasa rikici a tsakanin jama’a.
Sowore ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, inda ya amsa cewa ba shi da laifi.
Ana sa ran za a ci gaba da sauraron shari’ar a tsakiyar makon nan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment