Wata mummunar gobara da ta tashi a wani gini mai hawa uku a birnin Lucknow na ƙasar Indiya, ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 14, mafi yawansu ɗaliban jami’a ne.
Gobarar ta tashi ne a ranar Litinin a wani ginin kasuwanci da ke arewacin Indiya, wanda ke ɗauke da ɗakin karatu da kuma wurin koyar da zane-zanen kwamfuta (animation studio) da ɗalibai ke amfani da shi, tare da wani asibitin dabbobi.
Mahukunta sun ce gobarar ta fara ne daga bene na tsakiya na ginin, amma har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Mataimakin gwamnan jihar Uttar Pradesh, Brajesh Pathak, ya tabbatar da mutuwar mutanen, yana mai cewa galibin waɗanda suka mutu matasa ne. Wasu mutane huɗu kuma sun samu raunuka yayin da aka kai su asibiti.
Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wasu mutane ke ƙoƙarin tserewa ta tagogin ginin yayin da hayaki mai yawa ya mamaye wurin.
Jami’an kashe gobara sun tilasta shiga cikin ginin ta hanyar karya wani ɓangare na bango domin ceto mutanen da suka makale.
Wani ma’aikacin wurin zane-zanen kwamfutar ya bayyana cewa ma’aikata sun dawo daga cin abinci ne lokacin da suka lura da gobarar.
Ya ce da farko sun yi tunanin ƙaramar gobara ce, amma cikin kankanin lokaci hayaki ya cika ɗakuna da hanyoyin fita.
Jami’an kashe gobara sun yi amfani da kayan aiki na musamman domin rage hayaki da kuma nemo waɗanda suka makale.
Gobara a gine-gine na yawan faruwa a Indiya sakamakon rashin bin ƙa’idojin tsaro, matsalolin wayoyin lantarki, da ƙarancin kayan aikin kashe gobara.
Hukumomi sun fara bincike domin gano ainihin dalilin gobarar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment