Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK), ta ce ta ceto mutane 47, akasarinsu mata da yara, da mayakan ISWAP suka tsare a Kangarwa, karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Sojojin sun bayyana cewa an gudanar da aikin ceto ne a ranar 20 ga Yuni, 2026, yayin wani samame na hadin gwiwa da aka kai kan sansanonin 'yan ta'adda a yankin tafkin Chadi.
Mukaddashin Jami’in Yada Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Musa, ya ce an samu nasarar aikin ne sakamakon matsin lamba da hare-haren kasa da sama da sojoji suka ci gaba da kai wa kan 'yan ta'addan.
Ya ce hare-haren sun tilasta wa mayakan ISWAP barin maboyarsu cikin rudani, lamarin da ya bai wa wadanda aka yi garkuwa da su damar tserewa.
Rundunar ta kara da cewa mutanen da aka ceto suna samun kulawar likitoci a wani wuri mai tsaro, tare da tallafin jin kai domin taimaka musu wajen komawa rayuwa ta yau da kullum.
Sojojin sun sake tabbatar da aniyar ci gaba da kai hare-hare domin raunana kungiyar ISWAP da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

0 $type={blogger}:
Post a Comment