Gwamnatin Jihar Sokoto ta kaddamar da wani shiri da ya kunshi shugabannin al’umma daga dukkanin unguwanni 244 domin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara, tare da inganta allurar rigakafi.
An gabatar da shirin ne a wani taron horaswa da fadakarwa na tsawon kwanaki biyu da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Sokoto ta shirya.
Taron ya hada shugabannin kwamitocin ci gaban unguwanni, shugabannin mata da sauran masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 23 na jihar domin karfafa hadin gwiwar al’umma wajen inganta harkokin lafiya.
Daraktan Wayar da Kan Jama’a da Tallata Lafiya na hukumar, Dahiru Gada, ya bayyana cewa shugabannin unguwanni su ne hanyar hada hukumomin lafiya da al’ummomin karkara.
Ya bukaci shugabannin su kara karfafa gwiwar mata masu juna biyu su rika zuwa asibitoci domin duba ciki (antenatal) tare da haihuwa a wuraren lafiya karkashin kulawar kwararrun ma’aikatan lafiya.
Shirin ya kuma mayar da hankali kan lafiyar matasa, allurar rigakafi da kuma hana cututtuka kamar tetanus da diphtheria.
Mahukunta sun ce za a yi amfani da tsarin wayar da kan jama’a ta gida-gida domin kara samun damar kiwon lafiya da kuma rage mace-macen mata da yara a fadin Jihar Sokoto.

0 $type={blogger}:
Post a Comment