Wata kotu a jihar Katsina ta yanke ma wata matahukuncin kisa saboda taimaka wa ‘yan bindiga

Wata kotu a jihar Katsina ta yanke ma wata matahukuncin kisa saboda taimaka wa ‘yan bindiga

Wata Kotun Tarayya da ke Katsina ta yanke wa wata mata mai suna, Hauwa’u Mukhtar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da ya shafi ta’addanci.

An samu Hauwa'u Mukhtar da laifuka biyu da suka hada da hada baki wajen aikata ta’addanci da kuma taimakawa ayyukan ‘yan ta’adda.

An kama ta ne daga hannun jami’an Hukumar Tsaro ta DSS a ranar 16 ga Satumba, 2023, a tashar mota ta Jibia da ke Jihar Katsina, inda ake zargin ta na kokarin kai alburusai ga wani da ake zargi da kasancewa shugaban ‘yan bindiga ne.

Daga bisani DSS ta gurfanar da ita a gaban kotu.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a A.B. Bawale ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da laifukan da ake zargin ta da su ta hanyar hujjoji da kayayyakin shaida da kuma shaidun wadanda suka bayar da shaida a gaban kotu.

Kotun ta same ta da laifi kan dukkan tuhume-tuhumen da ake mata, sannan ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tanadin dokar laifuka ta Jihar Katsina ta shekarar 2021.

Wannan hukuncin ya zo ne makonni biyu bayan wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin hannu a harin da aka kai a Cocin Katolika ta St. Francis da ke Owo, Jihar Ondo, a shekarar 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 40.

0 $type={blogger}: