Ƙasar Argentina ta fara kare kambunta a gasar cin kofin duniya na 2026 da nasara, bayan ta doke Algeria da ci 3–0 a wasan rukuni na J.
Tauraron ƙasar Argentina, Lionel Messi, ya taka rawar gani inda ya zura ƙwallaye uku a raga, abin da ya ba ƙungiyarsa damar samun maki uku a wasan farko.
Wasan ya gudana ne a filin wasa na birnin Kansas da ke Missouri, inda Argentina ta nuna ƙwarewarta tun daga farkon wasa har zuwa ƙarshe.
Wannan wasan ya kasance na musamman ga Messi, wanda ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya bayan ya zama ɗan wasa na farko da ya buga gasar sau shida.
Messi, mai shekaru 39, ya kuma ci gaba da ƙara tarihi a fagen ƙwallon ƙafa bayan ya zama ɗaya daga cikin 'yan wasan da suka fi taka leda a matakin ƙasa da ƙasa.
Bayan wasan, Messi ya bayyana farin cikinsa da nasarar, inda ya baiyana godiya ga abokan wasansa da magoya bayan Argentina.

0 $type={blogger}:
Post a Comment