Wata Kotu a Indiya Ta Yi Watsi da Ƙarar da kamfanin Telegram ya shigar Kan Haramcin Amfani da Manhajar na wucin gadi da Gwamnatin indiya ta yi.

Wata Kotu a Indiya Ta Yi Watsi da Ƙarar da kamfanin Telegram ya shigar Kan Haramcin Amfani da Manhajar na wucin gadi da Gwamnatin indiya ta yi.

Wata kotu a Indiya ta yi watsi da ƙarar da manhajar aika saƙonni ta Telegram ta shigar domin kalubalantar dakatarwar wucin gadi da gwamnatin indiya ta sanya mata.

Babbar Kotun New Delhi ta yanke hukuncin ne bayan sauraron ƙara tsakanin jami'an gwamnati da wakilan Telegram. Indiya ta dakatar da manhajar ne bisa zargin cewa wasu tashoshi a cikinta suna sayar da tambayoyin jarabawar shiga makarantun likitanci da aka ce an fitar ba bisa ƙa'ida ba.

Ma'aikatar Fasahar Sadarwa ta Indiya ta ce ana amfani da wasu shafukan Telegram wajen yaɗa tambayoyin jarabawa, kuma ko da wasu bayanan na ƙarya ne, suna iya ruɗar ɗalibai.

Dakatarwar ta sa Telegram ta daina aiki a Indiya tare da cire ta daga wasu shagunan manhajoji. Wannan ya faru ne bayan da aka soke sakamakon jarabawar shiga karatun likitanci sakamakon zargin cewa an fallasa tambayoyin kafin lokaci.

Wanda ya kafa Telegram, Pavel Durov, ya soki matakin, yana cewa dakatarwar tana azabtar da miliyoyin masu amfani da manhajar maimakon waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Telegram ta ce ta cire sama da hanyoyin haɗi 900 da suka shafi abubuwan da ba su dace ba, amma gwamnati ta ce kamfanin bai ɗauki mataki cikin sauri ba.

Indiya ce babbar kasuwar Telegram, inda take da sama da masu amfani miliyan 150. Wannan rikicin ya zama ɗaya daga cikin manyan takaddama tsakanin babban kamfanin fasaha da gwamnatin Indiya a wannan shekara.

0 $type={blogger}: