Akalla mutane bakwai ne suka mutu bayan wasu bama-bamai biyu da aka dasa a gefen hanya sun tashi a yankin arewa maso yammacin Pakistan, a cewar jami’ai.
Bom na farko ya afka wa wata mota dauke da fasinjoji ne a ranar Asabar, yayin da na biyu ya tashi lokacin da masu ceto suka isa wurin domin taimakawa wadanda abin ya rutsa da su, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Wani jami’in ‘yan sanda a gundumar Bannu da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa, kusa da iyakar Afghanistan, ya ce an kai harin ne da wata na’ura mai fashewa da ake sarrafawa daga nesa (IED).
Ya ce wasu mutane uku sun jikkata yayin da ake kai su asibiti domin samun kulawar gaggawa, amma sai wani bam din ya sake tashi.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya yi Allah-wadai da harin tare da cewa gwamnati za ta tabbatar an hukunta wadanda suka aikata shi.
Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin. Sai dai kungiyoyin masu dauke da makamai, ciki har da Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP), na aiki a yankin.
Pakistan ta dade tana zargin gwamnatin Taliban ta Afghanistan da barin mayakan kungiyoyin dauke da makamai amfani da yankinta wajen kai hare-hare, amma Afghanistan ta musanta hakan.
Rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ya kara tsananta a ‘yan watannin nan, ciki har da hare-haren sama da arangama a kan iyaka.

0 $type={blogger}:
Post a Comment