Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation FANSAN YAMMA, ta ce ta ceto mutane 22 da aka yi garkuwa da su tare da dakile wasu hare-haren sace mutane a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na Jihar Sokoto.
Sojojin sun bayyana a cikin wata sanarwa ranar Asabar cewa an gudanar da ayyukan ne a ranar 18 ga Yuni, 2026, bayan samun bayanan sirri da kuma kiran neman agaji daga al’ummomin da lamarin ya shafa.
Jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce lamarin farko ya faru ne a hanyar Sabon Birni zuwa Shinkafi, a kauyen Kura Mota, inda ‘yan ta’adda suka tare hanya, suka kai hari kan motoci biyu na fararen hula tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji.
Ya ce an kashe wani farar hula yayin harin kafin sojoji su isa wurin su fara aikin ceto.
Danja ya bayyana cewa sojojin sun gaggauta kai dauki tare da taimakon jiragen sama wajen bibiyar wadanda suka kai harin.
Ya ce matsin lambar da sojojin suka yi ya tilasta wa ‘yan ta’addan barin wadanda suka sace tare da tserewa, inda aka samu nasarar ceto fasinjoji 17.
A wani samame na daban a wannan rana, sojojin sun amsa kiran neman agaji daga kauyen Chohi da ke karamar hukumar Isa, inda wasu ‘yan bindiga suka yi yunkurin sace manoma da ke aiki a gonakinsu.
Sojojin sun bi sawun maharan tare da ceto manoma biyar da aka yi garkuwa da su, inda daga bisani aka mayar da su ga iyalansu.
Rundunar ta kuma gudanar da sintiri a wasu kauyuka da suka hada da Gidan Rana da Gidan Sale domin kwantar da hankalin jama’a da hana sake aukuwar hare-hare.
Operation FANSAN YAMMA ta ce nasarar wannan aiki na nuna kudurin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da samar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment