Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja ya baiwa shugabannin Jami'an 'yan sanda na yankin Abuja mako guda domin su magance matsalar fashi a birnin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja ya baiwa shugabannin Jami'an 'yan sanda na yankin Abuja mako guda domin su magance matsalar fashi a birnin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ahmed Mohammed Sanusi, ya umarci Shugabannin ‘yan sanda na ƙananan hukumomi (DPO). da ke karkashin rundunar yankin babban birnin Tarayyar Abuja da su kawo karshen ayyukan fashi a tsakiyar birnin cikin mako biyu, ko kuma su fuskanci hukunci.

CP Sanusi ya bayar da wannan umarnin ne a yayin ganawa da DPOs guda 17 na yankin babban birnin Tarayyar Abuja a karshen mako.

Ya ce umarnin na da nufin duba halin tsaro da ake ciki tare da kara inganta dabarun yaki da sabbin barazanar tsaro a yankin.

Kwamishinan ya bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon karuwar matsalolin tsaro da suka hada da fashin titi, satar motoci, matsalar “one chance” da kuma tukin mota ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya kuma nuna damuwa kan ayyukan masu babura na kasuwanci a manyan hanyoyin birnin da lalata kadarorin gwamnati da na jama’a da ajiye motoci a kan manyan hanyoyi da kuma cunkoson ababen hawa.

Sanusi ya umurci Shugabannin 'yan sandan (DPOs) su tabbatar da kawo karshen wadannan laifuka cikin mako biyu, yana gargadin cewa jami’an da suka gaza cika umarnin za su fuskanci hukunci.

Ya umurci Babban Jami’in Yankin birnin da sauran DPOs su mayar da hankali wajen karfafa tsaro a tsakiyar birnin Abuja, yayin da shi da kansa zai kula da matsalolin tsaro a kewayen Abuja.

Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar ba za ta amince da sakaci ba, tare da umartar jami’ai su nuna kwarewa da tabbatar da bin umarnin.

Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da taimakawa ‘yan sanda ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

0 $type={blogger}: