“Aure ba ya cikin shirina” inji jarumar kannywood, Nafeesat Abdullahi.

“Aure ba ya cikin shirina” inji jarumar kannywood, Nafeesat Abdullahi.

Nafeesat, jarumar kannywood wacce ta fito a Matsayin Maimuna a shahararren shirin Hausa mai dogon zango mai suna Kaddara, ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ta bayyana ra’ayinta kan batun aure.

Jarumar ta bayyana cewa aure ba ya cikin shirinta na kashin kanta, inda ta tambayi dalilin da ya sa mace da ta yi kokari wajen gina rayuwarta da sana’arta da dogaro da kanta za ta koma karkashin ikon wani mutum bayan aure.

Maganganunta sun samu ra’ayoyi mabambanta, inda wasu suka soki kalaman nata, yayin da wasu kuma suka kare ta suna cewa tana da ‘yancin bayyana ra’ayinta.

Muhawarar ta fadada zuwa tattaunawa kan aure da rawar jinsi a cikin al’umma da zabin rayuwa da kuma tasirin shahararrun mutane ga jama’a.

0 $type={blogger}: