Wani Likita ɗan ƙasar Faransa ya kamu da cutar Ebola bayan aikin agaji a Congo.

Wani Likita ɗan ƙasar Faransa ya kamu da cutar Ebola bayan aikin agaji a Congo.

Faransa ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta farko a kasar bayan wani likita da ya dawo daga aikin agaji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DR Congo) ya kamu da cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Faransa ta bayyana a cikin sanarwa ranar Laraba cewa likitan yana aiki ne a wani yanki da cutar ke yaduwa.

Ma’aikatar ta ce: “Ana kula da majinyacin a wata babbar cibiyar lafiya karkashin tsauraran matakan kariya.”

Ta kara da cewa an dauki dukkan matakan da suka dace, ciki har da killace majinyacin da kai shi asibiti cikin tsaro domin hana yaduwar cutar.

Hukumomin lafiya sun fara binciken wadanda suka yi mu’amala da likitan domin gano mutanen da ka iya kamuwa da cutar. Wadanda aka gano za a bukace su su killace kansu na tsawon kwanaki 21.

Tun daga watan Mayu, lardin Ituri da ke arewa maso gabashin DR Congo ya zama cibiyar barkewar cutar Ebola, inda cutar ta kashe fiye da mutane 260 tare da kamuwa da sama da mutane 1,000 a kasar.

Haka kuma an samu rahoton bullar cutar a makwabciyar Uganda.

A ranar 17 ga Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana barkewar cutar a matsayin “gaggawar lafiyar jama’a da ta shafi kasa da kasa.”

Yawancin barkewar Ebola da aka taba samu a DR Congo sun kasance ne daga nau’in Ebola Zaire, amma wannan sabon barkewar yana faruwa ne daga nau’in Bundibugyo, wanda har yanzu babu ingantacciyar rigakafi ko magani da aka amince da shi.

0 $type={blogger}: