An Yankewa Mai Rajin Kare Haƙƙin Bil’adama, Mahrang Baloch Hukuncin rai da rai a Pakistan.

An Yankewa Mai Rajin Kare Haƙƙin Bil’adama, Mahrang Baloch Hukuncin rai da rai a Pakistan.

Wata kotun yaki da ta’addanci a Pakistan ta yanke wa fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Dr. Mahrang Baloch, da wani jagoran ƙungiyar Baloch Yakjehti Committee (BYC), hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari kan zargin kisan wani jami’in rundunar tsaro a lokacin wata zanga-zanga a watan Yulin 2024.

An tsare Mahrang Baloch tun watan Maris na 2025, kuma ta shahara wajen adawa da bacewar mutane ba tare da an san inda suke ba da kuma zargin take haƙƙin bil’adama a yankin Balochistan na kudu maso yammacin Pakistan.

Lauyan ta ya bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara a gaban babbar kotun Balochistan.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun soki yadda aka gudanar da shari’ar, inda suka ce an hana waɗanda ake tuhuma shiga shari’ar yadda ya kamata, tare da bayyana cewa an tilasta musu halarta ta hanyar bidiyo daga gidan yari.

Kotun ta ce ta samu Mahrang Baloch da abokin aikinta, Sibghatullah, da laifin kisa da wasu laifukan da suka shafi ta’addanci, tana mai cewa shaidu da bayanan likitoci sun goyi bayan tuhumar.

Gwamnan jihar Balochistan, Sarfaraz Bugti, ya ce hukuncin ya tabbatar da adalci ga sojan da aka kashe yayin zanga-zangar a birnin Gwadar.

Wani mai shirya ayyukan BYC, Lala Abdul Baloch, ya bayyana shari’ar a matsayin wadda ba ta da adalci, yana gargadin cewa hukuncin na iya ƙara fusata matasa a yankin.

Lauyoyin Mahrang Baloch sun ce za su kalubalanci hukuncin a kotu.

0 $type={blogger}: