Wata babbar kotun jihar Sokoto ta yanke wa wasu mutane uku, ciki har da wani ɗan ƙasar Nijar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin ta’addanci da safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗanda aka yankewa hukuncin su ne Yusuf Muhammad (wanda aka fi sani da Sallau), Jabbi Alhaji Yalle, da Kabiru Muhammad. An kama su ne a ranar 13 ga Yuni, 2025, daga hannun rundunar yaƙi da ta’addanci ta Hukumar DSS bisa zargin aikata laifukan da suka shafi ketare iyaka da safarar makamai, da ta’addanci.
A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Bello ya bayyana cewa an same su da laifukan da ake tuhumarsu da su, sannan ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace kuɗaɗen da aka samu a hannunsu a mayar da su ga gwamnatin tarayya.
Hukuncin na Sokoto ya zo ne bayan kusan mako guda da wata kotun tarayya da ke Katsina ta yanke wa wata mata mai safarar makamai, Hauwa’u Mukhtar, hukuncin kisa bayan DSS ta kama ta tana jigilar harsasai 438 zuwa ga wani da ake zargi da jagorantar ‘yan bindiga.
A baya, wasu mutane huɗu — Idris Abdulmalik Omeiza da Al Qasim Idris da Jamiu Abdulmalik, da Abdulhaleem Idris — an yanke musu hukuncin kisa a wata kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin hannu a hare-haren da suka yi sanadin mutuwar sama da masu ibada 40 a Owo, jihar Ondo.
Haka kuma, wata babbar kotun jihar Kogi da ke Lokoja ta yanke wa Jibrin Halilu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an same shi da laifin haɗa baki da satar mutane, da kisan wani mai otal a Obajana, jihar Kogi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment