Girgizar Kasa guda biyu masu Mai Karfin Maki 7.2 da maki 7.5 sun afka wa birnin Caracas na ƙasar Venezuela.

Girgizar Kasa guda biyu masu Mai Karfin Maki 7.2 da maki 7.5 sun afka wa birnin Caracas na ƙasar Venezuela.

Girgizar kasa mai karfi guda biyu sun afkawa Venezuela, inda suka jawo rushewar wasu gine-gine a babban birnin kasar, Caracas, tare da tayar da hankalin jama'a yayin da jami'an ceto ke neman wadanda suka makale.

Hukumar Binciken Kasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa girgizar kasar farko ta kai karfin maki 7.2, kuma cibiyarta tana yammacin garin Morón da ke bakin tekun Caribbean, kimanin kilomita 168 daga Caracas, a zurfin kusan kilomita 22 a karkashin kasa.

Bayan hakan, wata sabuwar girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta sake afkuwa cikin kankanin lokaci, lamarin da ya kara lalacewa da fargaba a yankin.

Hukumomi a yankin Chacao na Caracas sun ce akalla gine-gine hudu ne suka rushe, yayin da aka samu nasarar ceto mutane 18. Fiye da ma’aikatan ceto 500 ne ke aikin neman wadanda suka makale.

Mazauna birnin sun bayyana cewa an samu rudani da firgici, inda aka samu fashewar tagogi, tarwatsewar kayayyaki da tarkace a tituna. Wasu yankuna sun kuma rasa wutar lantarki da sadarwar intanet.

Masana kimiyyar kasa sun yi gargadin cewa ana iya samun karin girgizar kasa a kwanaki masu zuwa, ciki har da wasu masu karfin maki 3 zuwa 5.

Gwamnatin Venezuela ta umarci likitoci da ma’aikatan lafiya da su koma asibitoci da cibiyoyin gaggawa domin taimaka wa wadanda suka jikkata.

Kasashe daban-daban ciki har da Amurka sun mika sakon ta’aziyya tare da bayyana shirye-shiryen bayar da tallafi ga Venezuela yayin da ake ci gaba da aikin ceto da farfadowa.

0 $type={blogger}: