Manyan shugabannin kasashen Turai su biyar wadanda aka fi sani da E5 sun yi alkawarin nuna cikakken goyon bayansu ga ƙasar Ukraine a taron ƙungiyar NATO da za a gudanar a Ankara, babban birnin Turkiyya, a watan Yuli.
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce taron shugabannin ƙungiyar ƙasashe biyar na Turai (E5) da aka yi a Berlin na da nufin aika saƙo cewa Ukraine tana ci gaba da kasancewa mai ƙarfi duk da yaƙin da Rasha ke yi mata.
Taron ya haɗa shugabannin Jamus, Faransa, Italiya, Poland da Birtaniya domin shirin taron NATO na ranar 7 zuwa 8 ga Yuli.
Shugabannin Turai, ciki har da Emmanuel Macron da Giorgia Meloni da Donald Tusk da Keir Starmer, sun ce za su ƙara taimaka wa Ukraine ta hanyar takunkumi da matsin tattalin arziki kan Rasha, da taimakon ƙarfafa bangaren makamashin Ukraine.
Merz ya bayyana cewa samun nasara a taron NATO zai ƙara ƙarfafa dangantakar Turai da Amurka tare da haɗa kan ƙasashen Turai.
Wannan tattaunawa ta biyo bayan kiran bidiyo da shugabannin E5 suka yi da babban sakataren NATO, Mark Rutte.
Ana sa ran shugabannin ƙasashe 32 za su halarci taron NATO, ciki har da shugaban Amurka Donald Trump.
Haka kuma shugabannin Turai sun tattauna yiwuwar shiga aikin soji a mashigin ruwan Hormuz, amma sun ce hakan zai dogara ne kan yarjejeniyar da Amurka da Iran za su cimma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment