Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da shiyyar Zone 4 da ke Makurdi, Dankombo Morris, zuwa jihar Filato bayan mummunan harin da aka kai a ƙauyen Kawel da ke yankin Mushere, ƙaramar hukumar Bokkos.
An ce harin ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20 daga cikin mazauna yankin.
An ce tura jami’in na daga cikin matakan gaggawa domin duba halin tsaro a yankin, dawo da zaman lafiya da kuma hana sake faruwar irin wannan hari.
Sufeto Janar na ’Yan Sandan ya kuma amince da tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki, ciki har da rundunar Mobile Force da tawagogin musamman domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.
A lokacin ziyararsa a Bokkos, AIG Morris ya gana da shugabannin ƙaramar hukuma, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin tsara yadda za a magance matsalar.
Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos, Amalau Samuel Amalau, ya bayyana harin a matsayin mummunan laifi da aka aikata ba tare da dalili ba, inda ya nemi ƙarin jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugabannin mata a yankin sun kuma yi kira da a ƙara amfani da dabarun zamani wajen tsaron al’umma da kare wuraren da ke cikin haɗari.
AIG Morris ya isar da ta’aziyyar Sufeto Janar na ’Yan Sandan ga gwamnan Filato da al’ummar Bokkos, tare da tabbatar da cewa an tura ƙarin jami’ai domin dawo da kwanciyar hankali.
Ya buƙaci shugabannin al’umma da mazauna yankin su ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai masu amfani domin kama waɗanda suka aikata wannan hari da kuma tabbatar da zaman lafiya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment