Sojojin Najeriya Sun Ceto Fasinjoji 23 da Aka Sace a Hanyar Kogi

Sojojin Najeriya Sun Ceto Fasinjoji 23 da Aka Sace a Hanyar Kogi

Rundunar Sojin Najeriya sun ceto fasinjoji 23 da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka sace a kan hanyar Ayegunle-Bunu da ke Karamar Hukumar Kabba-Bunu a Jihar Kogi.

An gudanar da aikin ceto ne da sanyin safiyar Litinin, bayan jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun tare hanya, tare da sace matafiya a yankin.

Bisa bayanin hedikwatar sojoji, dakarun da ke yankin sun gaggauta isa wajen da lamarin ya faru domin fara aikin ceto, duk da cewa maharan sun tsere kafin isowarsu.

A yayin bincike a yankin, sojojin sun gano motocin bas guda biyu da kuma babbar mota kirar HOWO da aka bari a wurin.

Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu sun rasu yayin harin, yayin da wasu biyar suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti a Kabba domin samun kulawa.

Sojojin sun bayyana cewa matsin lamba da suka dinga yi wa ’yan bindigar ne ya tilasta musu sakin fasinjoji 23 da suka yi garkuwa da su, wadanda aka kubutar ba tare da rauni ba.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike da sintiri a dazukan da ke kewaye domin gano sauran wadanda ake zargin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, tare da kamo wadanda suka aikata harin.

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar tsaro a wasu sassan Jihar Kogi, inda ake yawan kai hare-hare kan matafiya da kauyuka.

Sojojin sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da yakar miyagun laifuka tare da kira ga jama’a da su rika bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen dakile ayyukan ’yan bindiga.

0 $type={blogger}: