Akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu yayin da sama da mutum 10 suka jikkata bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wajen wani taron murnar zagayowar ranar haihuwa a kauyen Gwon-Ajang da ke gundumar Foron, karamar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.
Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Lahadi lokacin da jama'a ke halartar bikin murnar zagayowar ranar haihuwan.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin wurin taron tare da bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici yayin da suka nemi mafaka.
Wani matashi daga yankin mai suna Bishop Iliya ya ce wadanda abin ya shafa sun taru ne domin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin abokansu lokacin da maharan suka kai farmaki.
“Mutanen suna cikin shagulgulan bikin ne lokacin da ‘yan bindigar suka iso suka fara harbin duk wanda suka gani. Wannan babban bala’i ne ga al’ummarmu,” in ji shi.
Kungiyar Berom Youths Moulder-Association (BYM-A) ta kuma tabbatar da faruwar harin, tana mai cewa akalla mutane takwas sun mutu yayin da sama da mutum 10 suka samu munanan raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Kungiyar ta yi Allah wadai da sabon tashin hankalin tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin dakile irin wadannan hare-hare da kuma kamo wadanda suka aikata laifin.
Rahotanni sun ce an kwashe wadanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya da ke kusa, yayin da jami'an tsaro suka bazama yankin bayan aukuwar lamarin.
Shugabannin al’umma sun nuna damuwa kan yawaitar hare-hare a wasu sassan Jihar Filato, suna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment