Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar da sabon jadawalin dawo da alhazan Najeriya daga Kasar Saudiyya, inda ta bayyana cewa jigilar alhazan zuwa gida zai fara ne daga ranar Laraba, 3 ga Yuni, 2026.
Tun da farko an tsara fara jigilar alhazan a wani lokaci na daban, amma hukumar ta ce an samu sauyin jadawalin ne sakamakon shirye-shiryen kamfanonin jiragen sama da kuma amincewar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA), wadda ke rarraba lokutan tashin jirage ga kamfanonin da ke gudanar da aikin hajji.
Shugaban Sashen Sufurin Jiragen Sama na NAHCON, Alhaji Habib Bello, ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama za su fara jigilar alhazai ne a lokuta daban-daban. Kamfanin Max Air zai fara jigilar alhazan Jihar Nasarawa ranar 3 ga Yuni, yayin da Flynas da Air Peace za su fara jigilar alhazan jihohin Ogun da Oyo daga ranar 4 ga Yuni.
Bello ya bukaci alhazai su bi ka’idojin kaya da aka tanada, inda aka amince da jakunkuna biyu masu nauyin kilo 23 kowannensu da kuma jakar hannu mai nauyin kilo 8.
Ya gargadi cewa rashin bin wannan ka’ida na iya haddasa jinkiri ko ma cire sunan mahajjaci daga jerin masu tafiya.
Ya kuma shawarci alhazai da su sanar da jami’an hajji aƙalla sa’o’i 48 kafin ranar tafiyarsu domin sauƙaƙa karɓar fasfo da duba kaya da kuma shirye-shiryen sufuri.
A nasa bangaren, shugaban Kwamitin Fasfo na Makkah, Alhaji Abdurrahman Mohammed, ya ce hukumar ta kammala matakin farko na ayyukan Hajjin 2026 kuma tana ci gaba da shirya fasfofin alhazan da za su dawo gida.
Ya bayyana cewa ana adana fasfofin alhazai a wurare masu tsaro domin kauce wa ɓacewa ko lalacewa, tare da tabbatar da cewa akwai hanyoyin magance matsalolin fasfo da suka ɓace ko samar da takardun tafiya na gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
NAHCON ta yi kira ga alhazai da jami’an jihohi da su ci gaba da ba da hadin kai domin tabbatar da cewa aikin dawo da alhazan Najeriya gida ya gudana cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment