Dakarun Rundunar Sojin Najeriya tare da goyon bayan Rundunar Sojin Sama sun samu nasarar ceto Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, bayan da wasu 'yan bindiga suka sace ta tare da mijinta makonni da suka gabata.
Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce an samu nasarar ceton ne sakamakon ƙoƙarin bincike da ceto da dakarun Operation Fansan Yamma suka ƙara kaimi wajen gudanarwa.
A cewarsa, dakarun sun yi artabu da 'yan bindigar a ƙauyen Tunga, inda suka samu nasarar kwato Hajiya Amina. A yayin artabun, 'yan bindigar sun harbe ta kafin su gudu sakamakon matsin lambar da sojojin ke musu.
An garzaya da ita zuwa asibitin sojoji domin kula da lafiyarta, kuma ana ci gaba da yi mata magani yayin da take samun sauƙi.
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ba ta da iyalanta dukkan tallafin da ake bukata, tare da ƙara kaimi wajen farautar waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma kawar da masu tada ƙayar baya a jihar Katsina da sauran sassan ƙasar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment