Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya, Yasser Al-Misehal, ya sanar da yin murabus bayan tawagar ƙasar ta kasa tsallake matakin rukuni a gasar cin kofin duniya na 2026.
Ƙungiyar kwallon kafar Saudiyya ta kammala gasar a matsayi na ƙarshe a rukunin H da maki biyu, bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Uruguay da kuma 0-0 da Cape Verde, kafin Spain ta doke ta da ci 4-0.
Al-Misehal ya ce ya ɗauki cikakken alhakin rashin nasarar tawagar, inda ya bayyana cewa sakamakon bai kai ga burin ƙasar ba.
Ya ce: “Rashin samun damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba bai dace da burinmu ba. Ina ɗaukar cikakken alhakin hakan, kuma ina ba da haƙuri ga duk waɗanda suka yi fatan ganin ƙungiyar ta yi abin da ya fi haka.”
Misehal, wanda ya jagoranci hukumar na tsawon shekaru bakwai, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Saudiyya na samun damar karɓar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2034, wani muhimmin shiri na ƙasar wajen rage dogaro da tattalin arzikinta kan man fetur.
Rashin nasarar Saudiyya a gasar ya zo ne bayan jerin sakamako marasa kyau a wasannin sada zumunci, lamarin da ya jawo korar kocin Faransa, Hervé Renard, wanda ya dawo karo na biyu jagorantar tawagar.
Saudiyya ta zuba makudan kuɗaɗe a harkar kwallon kafa a shekarun baya, inda ta jawo manyan ‘yan wasa kamar Cristiano Ronaldo da Neymar da Karim Benzema zuwa gasar Premier ta Saudiyya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment