Dan Wasan Kwallon Kafar Argentina Ya Rasa Matarsa Da ’Ya’yansa Biyu A Girgizar Kasar Venezuela.

Dan Wasan Kwallon Kafar Argentina Ya Rasa Matarsa Da ’Ya’yansa Biyu A Girgizar Kasar Venezuela.

Dan wasan kwallon kafar ƙasar Argentina, Lucas Trejo, ya rasa matarsa da ’ya’yansa biyu bayan mummunar girgizar kasar da ta afku a Venezuela.

Trejo, wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Club Sport Marítimo La Guaira da ke mataki na biyu a kasar, ya shafe kwanaki uku yana neman iyalansa a cikin baraguzan ginin gidansa da ya rushe, kafin jami’an ceto su gano gawar matarsa Yanina da ’ya’yansu Aaron da Ainhoa.

Lamarin ya faru ne bayan girgizar kasa mai karfin maki 7.2 da 7.5 a ma’aunin Richter ta afku a Venezuela a makon da ya gabata.

A lokacin da girgizar kasar ta faru, Trejo yana wani sansanin atisaye a Caracas, amma ya koma La Guaira cikin gaggawa, yankin da bala’in ya fi shafa.

Kungiyar Marítimo La Guaira ta bayyana bakin cikinta kan wannan babban rashi, inda ta ce tana tare da dan wasanta a wannan lokaci mai tsanani.

Dan uwan matar Trejo, Ricardo Ardiles, ya bayyana cewa dan wasan ya tarar da ginin da suke zaune ya koma tarkace, ba tare da samun wani abu ba.

Bala’in girgizar kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da barin wasu da dama babu labari. Haka kuma ya shafi harkar kwallon kafa a Venezuela, inda wasu matasa ’yan wasa suka rasa rayukansu.

Hukumar Kwallon Kafar Venezuela ta tabbatar da mutuwar matashin dan wasan kasar mai shekaru 18, Yimvert Berroteran, da kuma wasu ’yan wasa biyu, Víctor Palacios da Razan Sijaa.

Wani dan wasa mai suna Héctor Bello ma ya rasa abokiyar rayuwarsa, wadda rahotanni suka ce ta kare jaririnsu a lokacin da ginin ya rushe.

Har ila yau, wasu baki daga kasashe daban-daban, ciki har da Sinawa, sun rasa rayukansu sakamakon wannan bala’i yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

0 $type={blogger}: