Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, sun kai hari da safiyar yau Litinin 29 ga watan Yuni a makarantar gwamnati na jeka ka dawo da ke Lassa, ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno, inda suka kashe wani Malami tare da sace wasu ɗalibai da ke rubuta jarabawar NECO.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga makarantar da misalin ƙarfe 9 na safe, inda suka rika harbe-harbe a sama, lamarin da ya jawo firgici tsakanin ɗalibai da malamai da mazauna yankin. Daga bisani sun kashe wani malami tare da yin awon gaba da wasu daga cikin ɗaliban zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya ce har yanzu ba a gano wasu ɗalibai ba.
Ya ce: “Da misalin ƙarfe 9 na safe, wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun kai hari makarantar sakandare tare da yin harbe-harbe a sama.
A yayin harin, an sace wasu ɗalibai, yayin da wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba.”
Wannan hari ya faru ne kwanaki 47 bayan da ‘yan ta’adda suka sace ɗalibai 42, wasu daga cikinsu ƙananan yara ‘yan shekara biyu, daga makarantar Firamari na Mussa Primary da ƙaramar sakandire na Askira/Uba a ranar 15 ga Mayu, 2026, Inda har yanzu ba a sako waɗannan yaran ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment