Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce ta hallaka wasu ‘yan ta’adda da suka hada da manyan shugabanni a wani harin sama da ta kai a yankin Tafkin Chadi dake jihar Borno.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa an kai harin ne a sansanonin ‘yan ta’adda da ke yankin Arewacin Tumbuns, musamman a Metele da ke jihar Borno, wuri da aka sani da maboyar ‘yan ta’adda.
An gudanar da aikin ne karkashin Operation Hadin Kai, bayan samun bayanan leken asiri da binciken sa ido suka tabbatar da karuwar motsin ‘yan ta’adda a yankin.
Mai magana da yawun Rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai harin ne da sassafe a ranar Laraba, 10 ga Yuni, 2026, bayan samun sahihin bayanan sirri.
Ya bayyana cewa jiragen yakin sama sun gano tare da kai farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda da ke boye, inda rahoton bayan hari ya tabbatar da rusa wuraren tare da hallaka “dimbin ‘yan ta’adda.”
Hukumomin soji sun ce wannan farmaki na daga cikin kokarin da ake yi na dakile ayyukan ‘yan ta’adda da hana su kai hare-hare kan dakarun soji a yankin.
Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yaba da wannan nasara tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda lamba a fadin kasar.
Ya ce sojojin za su ci gaba da amfani da karfin jiragen sama wajen gano tare da rusa sansanonin ‘yan ta’adda, tare da hana su samun mafaka a Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment