Babbar Kotun Jihar Filato ta yanke hukunci cewa duk wani Bahaushe da aka haifa kuma ya taso a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, ya zama ɗan asalin yankin, muddin akwai alaƙar iyaye da yankin.
Mai shari’a C. Donglong na Kotun High Court 17 ne ya yanke hukuncin a shari’ar da Fatima Baba Akawu da mahaifinta, Baba Alhaji Akawu, suka shigar kan Karamar Hukumar Jos ta Arewa, saboda kin ba wa ‘yarsu takardar shaidar ‘yan asali.
Masu ƙara sun roƙi kotu ta bayyana ko ‘yar tasu da aka haifa a Jos ta Arewa, wadda mahaifinta ɗan asalin yankin ne, ta cancanci a ba ta takardar zama ‘yan asalin yankin duk da asalinta na kabilar Hausa.
Sun kuma yi korafin cewa an ba ta takardar zama (residential certificate) maimakon takardar ‘yan asali, abin da suka ce ya nuna wariya ne kuma ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
A hukuncin, kotu ta amince da dukkan buƙatun masu ƙara, inda ta ce hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da gaskiyarsu.
Mai shari’a Donglong ya bayyana kin ba wa ‘yar tasu, takardar ‘yan asali a matsayin wariyar ƙabila wadda ta saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotu ta kuma ce duk wani mutum da aka amince da shi a matsayin ɗan asalin Jos ta Arewa suna da ‘yancin samun takardar ‘yan asali, sannan ta soke amfani da takardar zama a maimakon takardar ‘yar asali, tana mai cewa ba ta da tushe a doka.
Haka kuma kotu ta hana Karamar Hukumar ci gaba da wannan dabi’a.
Mahaifin yarinyar, Baba Alhaji Akawu ya ce ya kai ƙara kotu ne bayan an hana ‘yarsa takardar ‘yan asali da take buƙata domin shiga jami’a, duk da cewa ta biya kuɗin da ake buƙata.
Ya ce an ba ta takardar zama ne kawai, yayin da wani mutum a rana ɗaya aka ba shi takardar ‘yan asali, abin da ya ce ya nuna wariya.
Ya yaba wa hukuncin kotun, yana mai cewa hakan ya ƙara tabbatar da cewa kotu ita ce mafakar talaka, kuma hukuncin zai zama abin koyi ga irin waɗannan matsaloli a faɗin ƙasar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment