China ta tabbatar da kama wani ɗan Amurka bisa zargin leƙen asiri

China ta tabbatar da kama wani ɗan Amurka bisa zargin leƙen asiri

Gwamnatin ƙasar China ta tabbatar da kama wani ɗan Amurka mai suna U Min Zin, inda ta ce ana zarginsa da aikata leƙen asiri da kuma barazana ga tsaron ƙasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta bayyana hakan ne a yau Juma’a ta bakin kakakinta Lin Jian, inda ya ce hukumomin China sun sanar da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Guangzhou game da kama mutumin.

Rahotanni sun nuna cewa an fara damuwa ne bayan bacewar ɗan Amurkan a birnin Kunming da ke kudu maso yammacin China a makon da ya gabata.

Hukumomin China ba su bayyana ƙarin bayani game da lamarin ba, amma sun ce yana da alaƙa da batun tsaron ƙasa.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin China da Amurka ke ci gaba da samun tashin hankali kan batutuwan tsaro da zargin leƙen asiri tsakanin ƙasashen biyu.

Har yanzu ba a ji martani daga hukumomin Amurka ba a lokacin da aka wallafa wannan labari.

0 $type={blogger}: