Gimbiya Bajrakitiyabha ta Ƙasar Thailand ta rasu tana da shekara 47 bayan shafe shekaru uku cikin suma.

Gimbiya Bajrakitiyabha ta Ƙasar Thailand ta rasu tana da shekara 47 bayan shafe shekaru uku cikin suma.

Gimbiya Bajrakitiyabha Mahidol ta ƙasar Thailand ta rasu tana da shekaru 47 bayan ta shafe kusan shekaru uku cikin suma sakamakon rashin lafiya mai tsanani, in ji Hukumar Fadar Masarautar ƙasar.

Gimbiya, wadda ita ce babbar ‘yar Sarki Maha Vajiralongkorn, ta rasu ne a ranar Alhamis da daddare a wani asibiti da ke birnin Bangkok, inda aka kwantar da ita tun bayan da ta faɗa cikin suma.

Sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da rasuwarta, tare da bayyana cewa ta dade tana fama da rashin lafiya mai tsanani a cikin shekaru uku da suka gabata.

Gimbiya Bajrakitiyabha ta shahara a Thailand saboda ayyukan hidimar jama’a da kuma aikinta a fannin shari’a, musamman ƙoƙarinta na inganta rayuwar mata a gidajen yari ta hanyar shirin ta na “Inspire” da ke mayar da hankali kan gyara halayen fursunoni da sake haɗa su cikin al’umma.

Ta kuma riƙe muƙamai daban-daban a fannin diflomasiyya da ƙasashen waje, ciki har da aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya kan Laifuka da Miyagun Kwayoyi, inda aka naɗa ta jakadiyar ƙwazo (goodwill ambassador) a shekarar 2017.

Fira Ministan Thailand, Anutin Charnvirakul, ya bayyana ta a matsayin “abin alfahari ga Thailand,” yana mai yaba mata kan jajircewarta wajen adalci da daidaito da ci gaban al’umma.

Masana sun ce an riƙa kallon gimbiya a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan gidan sarauta masu zamani da ke da kusanci da jama’a ta hanyar ayyukan jin ƙai da hidimar al’umma.

Bayan sanarwar rasuwarta, mutane da dama sun taru a Asibitin Tunawa da Sarki Chulalongkorn da ke Bangkok domin nuna alhini.

Rasuwarta ta kuma sake jawo magana kan batun gadon sarautar Thailand, kasancewar a baya ana ganin tana cikin masu yiwuwar gadon sarauta, duk da cewa tsarin ya kasance mai rikitarwa.

0 $type={blogger}: