Ƙasar Mexico wadda ke ɗaya daga cikin masu karɓar bakuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ta fara gasar cikin nasara bayan ta doke Afirka Ta Kudu da ci 2-0 a wasan buɗe gasar da aka buga a filin wasa na Mexico City.
Wannan wasa ya kasance sake haduwa mai tarihi, domin Mexico da Afirka Ta Kudu sun taɓa fafatawa a wasan buɗe gasar Kofin Duniya ta 2010, Inda suka sake haɗuwa a wannan karo na 2026.
Mexico ta nuna ƙwazo a wasan inda ta samu nasara sakamakon ƙwallaye da Julián Quiñones da Raúl Jiménez suka zura.
A gefe guda, Afirka Ta Kudu ta shiga matsala bayan da aka kori ‘yan wasanta biyu daga filin wasa, lamarin da ya rage ta da ‘yan wasa tara kacal har zuwa ƙarshen wasan.
Wannan nasara ta bai wa Mexico kyakkyawan farawa a gaban magoya bayanta, yayin da suke fatan yin tasiri a wannan gasa da ta faɗaɗa zuwa ƙasashe 48.
Gasar Kofin Duniya na FIFA 2026 wadda Mexico da Amurka da Kanada ke haɗin gwiwar karɓar bakuncinta za ta ƙunshi wasanni 104 kuma za ta ɗauki fiye da makonni shida ana fafatawa.
Mexico yanzu ta jagoranci rukuninta bayan wannan nasara ta ranar buɗe gasar, yayin da Afirka Ta Kudu za ta nemi dawo da martabarta a wasanninta na gaba domin ci gaba da fatan kaiwa matakin zagaye na gaba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment