Mutum 12 ne suka mutu a hatsarin jirgin sama a jihar Missouri na ƙasar Amurka.

Mutum 12 ne suka mutu a hatsarin jirgin sama a jihar Missouri na ƙasar Amurka.

Aƙalla Mutum 12 ne suka rasa rayukansu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a kusa da wani filin jirgin sama a jihar Missouri ta ƙasar Amurka a ranar Lahadi, in ji hukumomi.

Hukumar dake kula da sintiri a manyan hanyoyi jihar Missouri ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne kusa da filin Jirgin tunawa da Butler da ke garin Butler, da misalin ƙarfe 11:30 na safe agogon yankin.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin yana ɗauke ne da mutum 12, ciki har da matukin jirgin da fasinjoji 11, kuma dukkan su sun rasu a wajen hatsarin.

An tura jami’an agajin gaggawa daga hukumomi daban-daban, ciki har da ‘yan sandan jihar Missouri da ‘yan sandan Butler, da kuma ofishin sheriff na gundumar Bates, domin gudanar da aikin ceto da bincike a wurin da lamarin ya faru.

Hukumomi sun rufe wasu hanyoyin da ke kaiwa filin jirgin yayin da ake ci gaba da aikin agaji da bincike.

Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya haddasa hatsarin ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin.

Butler tana da nisan kusan mil 66 (kimanin kilomita 106) kudu da birnin Kansas.

0 $type={blogger}: