Farashin Tumatir Ya Tashi Zuwa N170,000 duk kwandon a Abuja.

Farashin Tumatir Ya Tashi Zuwa N170,000 duk kwandon a Abuja.

Mazauna Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, sun bayyana damuwa kan ci gaba da tashin farashin tumatir, lamarin da ke ƙara jefa iyalai da ‘yan kasuwa cikin wahala.

‘Yan kasuwa a manyan kasuwannin Abuja sun ce farashin tumatir ya ƙaru sosai cikin ‘yan makonnin da suka gabata. Babban kwandon tumatir da ake sayarwa tsakanin N85,000 da N90,000 a baya yanzu ya kai tsakanin N150,000 da N170,000.

Wani dillalin kayan lambu a kasuwar Suleja, Malam Isah Ado, ya ce ƙarancin tumatir a lokacin kaka, asarar amfanin gona bayan girbi, da tsadar sufuri daga gonaki zuwa kasuwanni ne suka haddasa hauhawar farashin.

A kasuwar Garki New Market kuwa, wata mai sayar da tumatir, Philomena Bassey, ta bayyana cewa tsadar jigilar kayan gona daga jihohin da ake nomansu zuwa Abuja na ci gaba da ƙaruwa, wanda ke sa farashin ya tashi.

Ta ce mutane da yawa suna zargin ‘yan kasuwa da neman riba mai yawa, alhali kuwa kuɗaɗen sufuri da sauran kashe-kashe ne ke ƙara tsadar kayan.

Ita ma wata ƙaramar ‘yar kasuwa da aka fi sani da Mummy Juli daga Kubwa ta ce ƙarancin tumatir ya sa farashinsa ya yi matuƙar tashi. Ta bayyana cewa a baya tana haɗa kwando ɗaya da wasu ‘yan kasuwa uku, amma yanzu dole ta haɗa da mutum biyar saboda tsadar sa.

Ta ƙara da cewa ƙaramin kwandon tumatir da take sayarwa tsakanin N4,000 zuwa N4,500 a baya yanzu yana kaiwa tsakanin N8,000 da N10,000.

A cewarta, tashin farashin ya sa ba za ta iya sayar da ƙaramin kaso na tumatir ƙasa da N1,000 ba, sabanin N100 da ake sayarwa a baya. Hakan ya jawo raguwar tallace-tallace saboda yawancin kwastomominta masu ƙaramin ƙarfi ne wajen samun kuɗi.

A bangaren masu saye kuwa, wata uwa mai yara biyu, Angela Ikenna, ta ce tsadar tumatir na ƙara nauyi ga kuɗaɗen abincin gidanta. Ta ce maimakon sayen tumatir na mako guda, yanzu tana sayen na kwana ɗaya ko biyu kawai.

Shi ma Moses Sunday ya bayyana cewa karin farashin tumatir na ƙara tsananta matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Wata mazauniyar Dei-Dei, Badia Muhammad, ta ce gidaje da dama sun fara komawa amfani da wasu kayan miya masu rahusa saboda tsadar tumatir.

Mazauna da ‘yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin da ke hana wadataccen samar da tumatir tare da ɗaukar matakan ƙara yawan amfanin gona domin rage tsadar sa a kasuwanni.

0 $type={blogger}: