Mutane sun fara komawa garuruwansu a kudancin Lebanon da aka lalata, yayin da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ke ci gaba da kasancewa cikin rauni

Mutane sun fara komawa garuruwansu a kudancin Lebanon da aka lalata, yayin da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ke ci gaba da kasancewa cikin rauni

A Kudancin Lebanon Iyalai da aka raba da muhallansu sun fara komawa garuruwansu da ƙauyukansu bayan sanar da tsagaita bude wuta da aka cimma tsananin Iran da Amurka, sai dai sun tarar da mummunar barna sakamakon watanni na Hare-haren Israi'la.

Gidaje, shaguna da gine-ginen jama’a sun lalace sosai sakamakon hare-haren kan iyaka da kuma luguden bama-bamai da Israi'la ta rinka yi, lamarin da ya sa wasu yankuna suka zama kamar ba a san su ba.

Mazauna da suka dawo daga wuraren mafaka da wuraren da suka fi aminci sun tarar da rufin gidaje da suka rushe, motoci da suka ƙone, da kuma gidaje da aka kwashe ƙofofi da tagogi.

Wasu iyalai suna komawa ne na ɗan lokaci domin ɗaukar muhimman takardu, tufafi da kayayyaki kafin su sake barin wurin. Wasu kuma, saboda rashin wani zaɓi, suna ƙoƙarin fara sabuwar rayuwa a cikin wannan ɓarnar.

An sanar da wannan tsagaita wutar ne bayan wani yarjejeniya ta farko tsakanin Amurka da Iran, amma har yanzu akwai rashin tabbas kan tsaro da kuma ko yarjejeniyar za ta dore.

Mahukuntan Lebanon sun ce hare-haren da Isra’ila ta kai sun kashe dubban mutane tare da tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu tun bayan ƙara tsananta rikicin.

Mazauna yankin sun ce suna fatan samun zaman lafiya, duk da irin ƙalubalen sake gina gidaje da al’ummominsu.

0 $type={blogger}: